Sudan : Ana Zanga Zangar Goyan Bayan El-Bashir
A Sudan daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zangar nuna goyan baya ga shugaban kasar Omar Hassan El-Bashir, a Khartoum babban birnin kasar.
Rahotanni daga kasar sun nuna cewa an zuba jami'an tsaro masu yawa domin bada kariya ga masu zanga zangar ta goyan bayan gwamnati.
Zanga zangar ta goyan bayan Al'Bashir, na zuwa ne bayan da shugaban ya zargi wasu da kisa boren nuna kiyaya ga gwamnatinsa.
Tun a ranar 19 ga watan Disamba da ya gabata ne al'ummar ta Sudan suka fara zanga-zangar kan tsadar rayuwa ta kalubalantar matakin gwamnatin kasar na kara farashin bredi da iskar gas, zangar zangar da daga bisani ta rikide zuwa ta kyammar gwamnatin Umar Hassan Al'Bashir tare da neman da ya sauka daga mulki.
Zanga zangar data barke a wasu biranen kasar ciki harda Khartoum, ta dai haddasa mutuwar mutane 19 a cewar hukumomin kasar ciki harda jami'an tsaro biyu.
Saidai wani rahoto da kungiyar kare hakkkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta fitar, ya nuna cewa mutum 37 suka mutu a zanga zangar, a yayin da MDD, ta bukaci da a gudanar da bincike marar bangaranci kan lamarin.