Mohamed Salah Ya Sake Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika
(last modified Wed, 09 Jan 2019 11:14:05 GMT )
Jan 09, 2019 11:14 UTC
  • Mohamed Salah Ya Sake Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika

Dan wasan kwallon kafa na kasar Masar Mohamed Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafan nahiyar Afirka na shekarar 2018, dan wasa na farko da ya lashe wannan lambar yabo shekaru biyu a jere.

An sanar da dan wasan na Liverpool, Mohamed Salah a matsayin wanda ya lashe kyautar ta 2018 a wani gagarumin biki da ya gudanaa a Dakar babban birnin Senegal .

Salah, ya yi takarar lashe wannan kyata ce da abokin taka ledarsa a Liverpool, wato Sadio Mane na Senegal da kuma Pierre-Emerick dan asalin Gabon da ke taka leda a Arsenal.

A shekara ta 2018, Salah ya jefa kwallaye 44 a wasanni daban daban da ya buga wa Liverpool, kuma a yanzu ya kasance dan wasa na farko daga arewacin Afrika da ya lashe kyautar sau biyu a jere.

Dama dai a jiya hukumar kwallon kafa ta Afirka ta sanar da cewa, kasar Masar ce za ta dauki bakuncin shirya gasar cin kofin kwallon kafan Afirka ta shekarar 2019, bayan data kwace ragamar hakan ga kasar Kamaru.