Zimbabwe : An Kashe Mutum Uku A Zanga zanga
(last modified Tue, 15 Jan 2019 15:42:23 GMT )
Jan 15, 2019 15:42 UTC
  • Zimbabwe : An Kashe Mutum Uku A Zanga zanga

Rahotanni daga Zimbabwe na cewa mutum uku ne aka kashe a zanga zangar data barke a kasar tun jiya Litini, biyo bayan matakin gwamnati na linka farashin man fetur a wannan kasa dake fama da matsalar tattalin arziki.

Bayanai da hukumomin kasar suka fitar sun ce mutum uku suka mutu a boren, wanda suka hada da wani jami'in 'yan sanda da aka hallaka a yankin Bulawayo, da kuma wani mutum guda a Chitungwiza dake kudancin birnin Harare, sai kuma mutumin guda da ya mutu a Kadoma dake tsakiyar kasar, kamar yadda kakakin 'yan sanda kasar, Charity Charamba, ya sanarwa manema labarai.

Ita mai dai babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta fitar da alkalumman makamtan wadanan amma a wasu yankunan, wanda ta ce na yucin gadi ne.

Da yake bayyana hakan kakakin jam'iyyar ta MDC, Jacob Mafume, ya ce akwai mutun biyu da suka mutu a yankin Chitungwiza sai kuma guda a Kadoma, tare da cewa akwai wasu mutane da dama da suka samu raunuka ciki harda wadanda suka samu munanan raunuka.

Da yammacin jiya ministan cikin gida na kasar, Owen Ncube, ya sanar da cafke mutrane kimanin 200 a mummunar zanga zangar data barke. 

Bayanai sun nuna cewa a yayin da aka shiga kwanan na biyu na yakin aikin da kungiyar kwadaga ta ZCTU ta kira, a yau Talata, 'yan sanda na sintiri a Harare babban birnin kasar, a yayinda kuma a cen birnin Bulawayo, dake zaman cibiyar 'yan adawa, jami'an tsaro sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga zangar.