Jan 15, 2019 16:42 UTC
  • Kenya : Harin Al'shebab Ya Kashe Mutum 5 A Nairobi

Kungiyar Al-shebab ta dauki alhakin kai wani hari data ce mayakan ta ne suka kai shi a Nairobi babban birnin kasar.

Rahotanni daga kasar dai sun ce an jiyo karan tashin bama-bamai da kuma harbe-harbe a wani otel dake birnin na Nairobi.

Wani bam ne ya fara tashi kafin daga bisani wani dan bindiga ya kusa kai cikin ginin otel din, kafin daga bisani ya fara harbi na kan mai uwa dawabi.

Har zuwa lokacin fasara wadanan labaren, babu cikakken bayani kan yawan mutanen da suka mutu ko wadanda suka jikkata, amma an fitar da mutane da dama da suka yi jina-jina daga cikin ginin.

A cikin wani gajeren sako na kungiyar ta al'shabab, da kamfanin dilancin labaren Shahaba ya fitar, kungiyar ta ce mayakan ne suka kaddamar da harin.

Tun dai bayan da sojojin Kenya suka sanya kafa a cikin watan Oktoba na 2011 a kasar Somaliya domin yakar kungiyar Al-shebab dake da alaka da kungiyar Al'Qaida, kasar ke fuskantar munanen hare-hare.

Idan ana tune a ranar 21 ga watan Satumban 2013, wani dan bindiga ya kai hari tare da yin garkuwa da mutane a cibiyar kasuwanci ta Westgate dake Nairobin inda mutane 67 suka mutu.

Tags