Mutane 20 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yan Bindiga A Tsakiyar Mali
(last modified Thu, 17 Jan 2019 11:54:56 GMT )
Jan 17, 2019 11:54 UTC
  • Mutane 20 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yan Bindiga A Tsakiyar Mali

Mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansu a lokacinda wasu yan ta'adda suka kai hari a kan wani kauye kusa da kan iyakar kasar Mali da Niger

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto jami'an tsaro na kasar Mali suna fadar haka a ranar Laraban da ta gabata, kan cewa yan bindiga sun kai hare-hare a kan garin Menaka da ke kan iyaka da kasar Niger, wanda ya kaiga mutuwar mutane akalla 20.

Bacu wa wani mutum ko wata kungiya wacce ta dauki nauyin alhakin kai wadannan hare hare. Sai dai an san cewa mayakan kungiyar Daesh a yankin sun dade suna kai irin wadannan hare-hare a yankin.

Rahoton MDD a shekara ta 2018 da ta gabata ya nuna cewa an kashe mutane akalla 500 a yankin tsakiyar kasar Mali sanadiyyar hare-haren yan ta'adda.