Fira Ministan Burkina Faso Ya Yi Murabus
Fira ministan Burkina Faso, Paul Kaba Thieba, ya yi murabus tare da sauren manbobin gwamnatinsa.
Mr Thieba, wanda kwarare ne kan sha'anin tattalin arziki, na shugabancin gwamnatin Burkina Faso tun a cikin watan Janairu na 2016, sai zuwa wannan lokaci da aka sanar da yin murabus dinsa.
Babu dai wani karin bayyani da akayi akan murabus din, wanda shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré ya sanar a cikin daren jiya Juma'a, a gidan talabijin kasar, amman shugaban ya gode wa fira ministan da sauren mambobin gwamnatinsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa sauren ministocin zasu ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za'a kafa sabuwar gwamnati.
A shekarun baya bayan nan dai Kasar Burkina Faso, na fama da matsalar tsaro mai nasaba da hare haren mayakan dake ikirari da sunan jihadi, da kuma bore na al'ummar kasar dake son zama gwani kalubale ga gwamnatin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa garkuwa da mutane da ake musamman 'yan kasashen waje da kasar ke fuskanta, na daya daga cikin koken koken da wasu 'yan kasar ke yi tare da bukatar fira ministan kasar Paul Kaba Thieba, da ministan tsaron kasar su yi murabus.
A ranar 31 ga watan Disamba da ya gabata an kafa dokar ta baci a sassan kasar da dama.