Senegal : 'Yan Takara 5 Zasu Fafata A Zaben Shugaban Kasa
(last modified Mon, 21 Jan 2019 04:01:26 GMT )
Jan 21, 2019 04:01 UTC
  • Senegal : 'Yan Takara 5 Zasu Fafata A Zaben Shugaban Kasa

Kotun tsarin mulki a Senegal, ta fitar da jerin sunayen 'yan takaran da zasu fafata a zaben shugaban kasar na watan fabrairu mai zuwa.

'Yan takara biyar ne zasu fafata a zaben, ciki har da shugaba mai barin gado Macky Sall.

Sauren 'yan takaran hudu sun hada da Idrissa Seck na jam'iyyar Rewmi, da Usman Sonko na Pastef, sai Elhaji Issa Sall na jam'iyyar  PUR, da kuma Me Madicke Niang na kawancen Madicke 2019. 

Saidai kotun bata amince da takara wasu sananun fuskoki  'yan siyasar kasar ba, da suka hada da tsohon magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, wanda ake tsare da gidan kurkuku, da kuma Karim Wade, wanda da ne ga tsohon shugaban kasar Abadulaye Wade.

Bangarorin jam'iyyun siyasa na 'yan takaran biyu da akayi watsi dasu sun ce zasu ci gaba da fafatuka a fagen siyasa, saidai ba tare da yin karin haske ba kan mi abunda hakan yake nufi.

A Ranar 24 ga watan Fabrairu ne za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Senegal.