D.R Congo : Kungiyoyin EU Da AU, Zasuyi Aiki Da Tshisekedi
Kungiyar tarayya Turai (EU), da takwararta ta Afrika (AU), sun ce a shirye su ke su yi aiki da zababen shugaban kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, Felix Tshisekedi.
Bangarorin biyu sun bayyana hakan ne, bayan da a cen baya suka nuna shakku kan nasarar da dan takaran Felix Tshisekedi, ya samu a zaben shugaban kasar na ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata.
Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai, tare da babbar jami'ar diflomatsiyya ta kasashen turai, a birnin Brussels a daura da taron ministocin harkokin waje na kasashen nahiyoyin biyu, wakilin kungiyar ta (AU), Smaïl Chergui, ya ce a shirye muke a matsayin kungiyar tarayya Afrika, muyi aiki da shugaba Tshisekedi da kuma dukkan sauren bangarorin kasar ta Congo.
Ita kuwa Mme Mogherini, cewa tayi sun na'am da sakamakon zaben, amma shugaban ya zamo mai hada kan jama'a, ya kuma nemi yin tattaunawa da dukkan bangarori na cikin gida.
Ta kara da cewa al'ummar Congo sun yi zabinsu na samun canji, don haka kalubalen dake gaban sabon shugaban, shi ne matsalar tsaro, tattalin arziki da kuma mulki na gari domin biyan bukatun al'umma.
Kungiyar ta EU ta ce babbar abokiyar huldar DR Congo ce, kuma zata ci gaba da kasancewa hakan, tare da bukatar kasar ta Congo data maido da wakilin kungiyar dan asalin kasar Belgium da hukumomin kasar suka kora a karshen watan Disamba.