Mali : (AU) Ta Yi Allah Wadai Da Hari Kan Tawagar MINUSMA
(last modified Wed, 23 Jan 2019 10:58:01 GMT )
Jan 23, 2019 10:58 UTC
  • Mali : (AU) Ta Yi Allah Wadai Da Hari Kan Tawagar MINUSMA

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU), Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da ya kashe sojojin kasar Chadi 10 dake aikin kiyaye zaman lafiya karkashin tawagar MINUSMA a kasar Mali.

Harin wanda ya abku a ranar Lahadin da ta gabata, a garin Aguelhok dake yankin Kidal na kasar Mali, ya kuma jikkata a kalla wasu sojoji 25.

Bayan da sakon ta'aziya da ya aikewa gwamnatin Chadi da iyalan wadanda suka rasa rayuka, shugaban hukumar gudanarwar ta AU ya bukaci hukumomin kasar Mali da kungiyoyin 'yan tawaye da suka sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kasar, da su yi kokarin zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki don hukunta su.

Faki ya bayyana fatansa na ganin wadanda suka ji rauni sun samu sauki cikin sauri, Ya kuma gode musu a madadin daukacin jama'ar nahiyar Afirka a bisa jaruntan da suka nuna.