Mutum 97 Ne Ke Zawarcin Kujerar Shugaban Kasa A Aljeriya
(last modified Fri, 25 Jan 2019 11:48:05 GMT )
Jan 25, 2019 11:48 UTC
  • Mutum 97 Ne Ke Zawarcin Kujerar Shugaban Kasa A Aljeriya

Ma'aikatar cikin gidan Aljeriya ta sanar da cewa ya zuwa yanzu kimanin mutum 97 ne suka ajiye takardun neman shugabancin kasar cikin kuwa harda 'yan takara 12 na jam'iyun kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto ma'aikatar cikin gidan Aljeriya na cewa bisa dokokin Aljeriya, duk wanda yake son tsayawa takarar shugaban kasa, to dole ne ya ajiye takardunsa kafin  kwanaki 45 na fara tattance 'yan takara daga bangaren  hukumar zaben kasar, kuma ya zuwa yanzu kimanin mutum 97 ne suka ajiye takarun takarar su a ma'aikatar cikin gidan kasar.

Tun a shekarar 1999 ne shugaba mai ci Abdelaziz Bouteflika ya hau kan ragamar milkin kasar ta Aljeriya, inda a yayi wa'adin milki har so hudu a jere, amma duk da hakan wasu jam'iyu da manyan kasar na bukatar ya ci gaba da zama a kan karagar milkin kasar.

Manyan jam'iyu biyu da suka hada da Tahrirul-watani da tajamu'ul watani Adimokaradiya, duk da cewa ba su gabatar da 'yan takararsu a hukumance ba, to amma a baya sun sha nuna goyon bayansu ga shugaban mai ci.

Masu sharhi kan siyasar kasar ta Aljeriya, na ganin cewa babu wani dan takara da zai iya karawa da shugaba Abdelaziz Bouteflika matukar dai ya tsaya takara a kasar.