An Sabunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Jihohi Biyu Na Sudan
Shugaban kasar Sudan ya sabunta yarjejjeniyar tsagaita wuta a jahohin Nile Aby da Kurdufan ta kudu.
A wannan Talata ce Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ya sanar da yarjejjeniyar tsagaita buda wuta a jahohin Nile Aby da kurdufan ta kudu.
Tun a shekarar 2011 ne kungiyoyin dake dauke da makamai a yankunan Kurdufan ta kudu da Nile Aby bayan da aka sanar da samun 'yancin Sudan ta kudu,.
A yayin da ya ziyarci wadannan jahohi, shugaba Al-bashir ya ce abinda ya sanya gabansa a halin da ake ciki yanzu dawo da cikekken sulhu da tsaro a wadannan yankuna.
A bangare guda kuma kungiyar ma'aikatan kasar ta bukaci a gudanar da zanga-zangar gama gari na nuna adawa da karin kudin man fetir da hauhawar farashin kayan masarufi a kasar.
Tun daga ranar 19 ga watan Dicembar 2018 din da ta gabata ce, Al'ummar kasar Sudan suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da karin kudin Man fetir, da hauhawar farashin kayan masrufi ciki harda biredi a kasar.