Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Shugaba Maduro
Ma'aikatar harakokin kasashen wajen Venezuela ta sanar a jiya laraba cewa kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasar mai ci Nicolas Maduro
Ma'aikatar harakokin kasashen wajen Venezuela ta nakalto jakadan kasar a kasar Ethiopia na cewa a jiya laraba mataimakin kungiyar tarayyar Afirka Thomas Kwesi Quartey ya nuna goyon bayan kungiyar AU ga Al'ummar kasar Venezuela da kuma zababben shugaban kasar Nicolas Maduro.
Kafin hakan dai wakilin kasar Afirka ta tsakiya a MDD Jerry Matjila ya nuna goyon bayan kasarsa ga shugaban kasar ta Venezuela mai ci Nicolas Maduro.
A cikin watan Mayu na shekarar 2018 da ta gabata ne dai aka zabi Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasa.
A makon da ya shude ne dai shugaban Majalisar dokokin kasar ta Venezuela Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar, lamarin da ya bude sabon shafin dambaruwar siyasa a cikin kasar
Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ministansa na harkokin wajen Mike Pampeo sun nuna cikakken goyon bayansu ga Juan Guaido tare da daukarsa a matsayin shugaban kasa tare da kakaba sabbin takunkumai kan gwamnatin Shugaba Maduro domin ci gaba da yi masa matsin lamba na ya mika mulki, matakin da kasashen da suka hada da Rasha da China suka danganta da shishigi na wuce gona da iri na Amurka a cikin al'amurran cikin gida na kasar ta Venezuela.
Saidai a bangare guda, wasu kasashen turai da suka hada da Faransa, Jamus, Spain, Burtaniya, Portugal, da Holland sun baiwa shugaba Maduro wa'adin kwanaki takwas na ya kira zabe ko kuma su amince da Juan Guaido.