Mali : Yawan 'Yan Gudun Hijira Ya Linka Sau Uku
(last modified Fri, 01 Feb 2019 04:25:44 GMT )
Feb 01, 2019 04:25 UTC
  • Mali : Yawan 'Yan Gudun Hijira Ya Linka Sau Uku

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan 'yan gundun hijira a Mali, ya linka har sau uku a cikin shekara guda, saboda matsalar tsaro a iyakar kasar da Burkina Faso.

Rahoton na MDD, ya nuna cewa, rabin 'yan gudun hijiran da suka kai kimanin 120,000 suna a jihar Mopti ne, kuma mafi akasarinsu sun tsere daga yankin kudancin kasar mai iyaka da Burkina Faso inda suka nemi mafaka a wasu sassan jihar.

A cewar MDD, mutanen na gujewa rikice rikicen masu nasaba da kabilanci, kuma kashi 1/3 na mutanen sun bar gidajensu tsakanin watan Satumba da Disamba na shekara data gabata.

MDD ta kuma nuna damuwa akan mawuyacin halin da 'yan gudun hijiran ke ciki musamman a daidai wannan lokaci da yanayi ke sauyawa cikin sauri zuwa zafi a wannan yankin, duba da yadda kusan kashi 80% na filayen noma a yankin Sahel sun lalace, wanda kuma dama da noma da kiwo ne mutanen yankin ke rayuwa.

Ko baya ga hakan a cewar MDD, kasar Mali na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro mai nasaba da gungun mayaka wanda sannu a hankali ke bazuwa daga arewa zuwa tsakiyar kasar, da kuma kan iyakokinta da kasashen Nijar da Burkina faso.