Feb 02, 2019 17:36 UTC
  • CAF U20 : Nijar Da Afrika Ta Kudu Sunyi Kunnen Doki 1 - 1

An bude gasar cin kofin Afrika ta 'yan kasa da shekara 20, wacce kasar Nijar ke karbar bakunci a bana.

A karawar farko da akayi tsakanin tawagar kwallon kafa ta Nijar mai masabkin baki da ta Afrika ta Kudu, an tashi kunnen doki 1 -1 a wasan da suka guda kammala a dazu dazu.

Yanzu haka dai ana cikin karawa tsakanin tawagar kwallon kafa ta Najeriya da kuma Burundi.

Zuwa gobe Lahadi akwai karawa tsakanin Senegal da Mali, sai kuma karawa ta biyu tsakanin Burkina Faso da Ghana.

Tags