An Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Senegal
Feb 03, 2019 09:55 UTC
A Senegal, yau Lahadi ne aka fara yakin neman zaben shugaban kasar na ranar 24 ga watan Fabrairu nan a hukumance.
'Yan takara biyar ne zasu fafata a zaben mai zuwa da suka hada da shugaban kasar mai barin gado, Macky Sall, Idrissa Seck, Issa Sall, Madicke Niang da Usman Sonko.
A ranar 22 ga watan nan ne, wato kwanaki biyu kafin kada kuri'a za'a kammala yakin neman zaben.
Wasu daga cikin sanannun fuskoki na 'yan siyasar kasar da suka hada da tsohon magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, da kuma dan tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade cewa da Karim Wade basu samu damar shiga zaben ba, kasancewar kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da takararsu.
Tags