Feb 03, 2019 10:11 UTC
  • AFCONU20 : Najeriya Ta Lallasa Burundi 2 - 0

A gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 20, da aka fara jiya Asabar a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta tarayyar Najeriya, ta lallasa ta Burundi da ci 2-0.

A karawar farko da akayi har wa yau a jiyan, kasar Nijar mai masabkin baki ta yi kunnen doki da Afrika ta Kudu, 1 -1 a wasan da suka buga babban filin wasa na Yamai.

Yau Lahadi akwai karawa tsakanin Senegal da Mali, sai kuma karawa ta biyu tsakanin Burkina Faso da Ghana.

 

Tags