Kawancen Jam'iyyu Masu Mulki Sun Goyi Bayan Takara Bouteflika
(last modified Sun, 03 Feb 2019 11:00:05 GMT )
Feb 03, 2019 11:00 UTC
  • Kawancen Jam'iyyu Masu Mulki Sun Goyi Bayan Takara Bouteflika

Kawancen Jam'iyyun siyasa guda hudu dake mulki a kasar Aljeriya, sun nuna goyansu a hukumance kan takara shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika a zaben shugaban kasar.

A sanawar da suka fitar gungun Jam'iyyun da suka hada da FLN, RND, TAJ, da MPA na nema ga shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, da ya tsaya takara a zaben shugabancin kasar dake tafe, domin neman wani wa'adin mulki a karo na biyar.

Kawo yanzu shugaba Buteflika, bai bayyana sha'awarsa ba ta sake tsayawa takara a zaben, a yayin da ya rage wata guda a je babban zaben na ranar 18 ga watan Afrilun wannan shekara, duk da cewa fira minstan aksar ya bayyana a wani taron manema labarai cewa babu wata tantama akan takara shugaban kasar mai shekaru 81.

Masu sha'awar tsayawa takara a zaben nada har zuwa ranar 3 ga watan Maris domin ajiye takardun takararsu a zaben.