Feb 07, 2019 12:38 UTC
  • Malaman Makarantu Sun Yi Zanga-zanga Akan Karancin Albashi

A jiya Laraba ne malaman makarantu a kasar Tunisiya su ka gudanar da Zanga-zangar yin kira da a kara musu albashi

Malaman da suka cika wasu tituna na birnin Tunis sun daga kwalaye da suke dauke da bayanai akan tsanantar matsalolin tattalin arziki a kasar suna masu bukatar a yi musu karin albashi.

Masu Zanga-zangar sun bayyana cewa a lokaci mai tsawo suna da sabani da ma'aiaktar ilimi ta kasar akan batutuwa da dama da su ka hada da karancin albashi da kuma yanayi koyarwa a makarantun kasar

Yin Zanga-zanga akan tsanantar matsalar tattalin arziki a kasar Tunisiya ta yawaita a cikin watannin bayan nan.

"Yan adawar siyasa suna zargin gwamnatin Pira minista Yusuf Shahid da gajiyawa wajen warware matsalar tattalin arzikin kasar.

Tags