Wade Ya Yi Kiran Kauracewa Zaben Senegal
(last modified Fri, 08 Feb 2019 03:12:31 GMT )
Feb 08, 2019 03:12 UTC
  • Wade Ya Yi Kiran Kauracewa Zaben Senegal

Tsohon shugaban kasar Senegal, Abdulaye Wade ya sake nanata kiran a kauracewa babban zaben kasar na ranar 24 ga watan nan na Fabrairu.

Tsohon shugaban, dake da zama a Faransa, ya bayyana hakan ne bayan da koma gida a jiya Alhamis.

Mista Wade, dai na zargin cewa an riga an shirya komi yadda shugaban kasar Macky Sall zai yi tazarce a zaben shugaban kasar dake tafe.

Wade, ya kuma bukaci sauren 'yan takara zaben shugaban kasar hudu da zasu fafata da shugaban mai barin gado dasu kauracewa zaben.

Ya kara da cewa tini Macky Sall, yana rike da sakamakon zabensa, kashi 55% ko kuma 65%, a don haka ya kuma kira al'ummar kasar dasu kauracewa zaben.

Tsohon shugaban ya kuma ce zai shirya ganganmi da zanga zanga a duk fadin kasar, gabani da lokacin zabe da kuma bayansa tare da kiran a kona katinan zabe, tare da kira ga jami'an tsaro da kada su murkushe masu zanga zangar ko kuma yin amfani da hayaki mai sa hawaye kansu.

Yan takara biyar ne zasu fafata a zaben kasar ta Senegal, na ranar 24 ga wata nanm wadanda suka hada da shugaban kasar mai barin gado, Macky Sall, da Idrissa Seck, da Issa Sall, da kuma Madicke Niang sai Usman Sonko.

Saida wasu daga cikin sanannun fuskoki na 'yan siyasar kasar da suka hada da tsohon magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, da kuma dan tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade cewa da Karim Wade basu samu damar shiga zaben ba, kasancewar kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da takardun takararsu.