Aljeriya : FLN, Ta Tsaida Buteflika A Matsayin Dan Takaranta
Jam'iyyar FLN, mai mulki a Aljeriya, ta sanar da tsayar da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a babban zaben kasar dake tafe.
Jam'iyyar ta bayyana hakan ne birnin Alger a yayin babban gangaminta na gabanin yakin neman zabe.
Dama dai a makon da ya gabata, kawancen Jam'iyyun siyasa guda hudu dake mulki a kasar, sun nuna goyansu a hukumance kan takara shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika a zaben mai zuwa.
Wannan shi ne karo na biyar da jam'iyyar ta FLN dake mulkin wannan kasa ta Aljeriya tun bayan samun 'yancin kanta ke tsaida, Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasa.
A ranar 18 ga watan Afrilu na wannan shekara ne al'ummar kasar ta Aljeriya ke kada kuri'a a babban zaben kasar, saidai har yanzu shugaban mai shekaru 81, wanda baida cikakar lafiya bai bayyana aniyarsa ba, ta sake tsayawa takara a zaben ba.
A ranar 3 ga watan Maris mai zuwa ne za'a rufe karbar takardun masu sha'awar tsayawa takara a zaben kasar.