Al'Sisi Na Masar Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar AU
(last modified Sun, 10 Feb 2019 10:01:01 GMT )
Feb 10, 2019 10:01 UTC
  • Al'Sisi Na Masar Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar AU

Shugaban kasar Masar, Abdel fatah Al-Sisi, ya karbi shugabancin kungiyar tarayya Afrika na wannan karo a hukumance, daga hannun takwaransa na Ruwanda Paul Kagame.

Daga cikin batutuwan da sabon shugaban kungiyar Abdel Fatah Al-Sisi, zai sa a gaba akwai matsalar tsaro da yaki da ta'addanci da kuma halin da kasar Libiya ke ciki da kuma yarjejeniyar nan ta cinikaya marar shinge tsakanin kasashen na Afrika da har yanzu take tangal-tangal.  

Kafin hakan dama shugaban hukumar Tarayyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, su matsa kaimi wajen tabbatar cimma yarjejeniyar.

Jiya ne dau shuwagabannin kasashen Afrika, suka fara taronsu na shekara-shekara, karo na 32 a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha.