Shugaban Kasar Algeriya Zai Nemi Shugabancin Kasar A Karo Na Biyar
(last modified Sun, 10 Feb 2019 19:20:19 GMT )
Feb 10, 2019 19:20 UTC
  • Shugaban Kasar Algeriya Zai Nemi Shugabancin Kasar A Karo Na Biyar

Shugaban kasar Algeriya Abdul'aziz Butaflika zai tsaya takarar neman kujerar shugabancin kasar Algeriya karo na biyar duk tare da rashin lafiay da yake fama da ita.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran APS na gwamnatin kasar ta Algeriya yana  fadara haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa shugaban dan shekara 81 a duniya wanda kuma yake kan kujerer shugabancin kasar tun shekara ta 1999 zai tsaya takarar shugabancin kasar karo na biyar.

APS ya kara da cewa shugaban Abdulazizi ya ce zai gudanar da wata gagrumar taro na tattauna matsalolin tattalin arziki, siyasa da kuma  zamnatakewa a kasar ta Algeriya don magance dukkan matsalolin a wadannan fagaggen.

Shugaba  Abdul-aziz dai baya iya tashi tsaye tun bayan da wasu gabban jikinsa suka shanye a shekara ta 2013, amma masu goyon bayansa sun bayyana cewa rashin lafiyarsa ba zai hana shi aikin shugabancin kasar ba. 

Tun lokacinda rashin lafiyar ta same shi dai a daina ganin shugaban a cikin jama'a, don yana zaune ne a kan keken guragu tun lokacin. 

Wasu jam'iyyun adawa a kasar ta Aljeriya dai sun haramta zaben na waten Afrilu mai zuwa, don suna ganin ba zabe za'a yi ba. Za'a dai bayyana shugaba abdul-aziz a matsayin wanda ya lashe zaben.