Nijar : Bazoum, Ne Dan Takaran Jam'iyya Mai Mulki A Zaben 2021
(last modified Mon, 11 Feb 2019 04:06:24 GMT )
Feb 11, 2019 04:06 UTC
  • Nijar : Bazoum, Ne Dan Takaran Jam'iyya Mai Mulki A Zaben 2021

Jam'iyyar PNDS-Tarrayya, mai mulki a Jamhuriya Nijar, ta tsaida Mal. Mohammed Bazoum, a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasar na 2021 idan Allah ya kai.

Jam'iyyar ta yanke shawara tsaida Mal. Mohamed Bazoum, wanda shi ne ministan cikin gida na kasar a zaben na 2021, a yayin wani taron kwamitinta na zartawa da yammacin jiya Lahadi a Yamai babban birnin kasar.

Mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar sun shaida wa masu aiko da rahotanni cewa, an amince da tsaida ma. Bazoum da gagarimin rinjaye, wanda kuma a cewarsu ya kawo karshen cece-kucen da ake na cewa jam'iyyar na fama da rikicin cikin gida.

Mal. Bazoum wanda yana daga cikin wadanda suka kafa wannan jam'iyya, ya kasance a tsawan shekaru na hannmun daman shugaban kasar mai ci Alhaji. Isufu Mahamadu, wanda wa'adin mulkinsa na biyu ke kawo karshe a shekara 2021.

Bayan zabensa a waccen lokacin ne ya mika ragamar mulkin jam'iyyar ta PNDS-tarayya ga Bazoum Mohamed.

Tsaida Mohammed Bazoum a zaben shugaban kasa na 2021, na zuwa ne 'yan kwanaki kadan, bayan da shugaban kasar ya kori ministan kudinsa, kana sakatare janar na jam'iyyar, Mal. Hasumi Masaoudu, wanda aka ce ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takara a zaben mai zuwa.

A yanzu dai yayin da ya rage, shekaru biyu a je zaben shugaban kasar, Mal. Mohammed Bazoum, wanda tsohon malamin falsafa ne, haifafen garin Tesker na jihar Zinder, jan aikin dake gabansa shi ne yin aiki tukuru na ganin jam'iyyar dake mulkin kasar tun shekara 2011, ta ci gaba da jan ragamar mulkin kasar, bayan shekaru na adawa.