Rikicin Gabanin Zabe Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Senegal
Jami'an tsaron Jandarma a Senegal, sun cafke mutane 24, bayan wani rikicin gabanin zabe da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla uku a garin Tambacounda dake gabashin Dakar babban birnin kasar.
Bayanai sun nuna cewa daga cikin mutanen da aka kama kimanin ashirin daga cikinsu maboya bayan jam'iyyar PUR ce ai adawa.
Mai shigar da kara na gwamnatin yankin, Demba Traoré, ya ce jami'an tsaro sun kama makamai da suka hada da wukake daga hannun magoya bayan jam'iyyar ta PUR.
Shugaban jam'iyyar ta hammaya Issa Sall, ya sanar a shaffinsa na twitter cewa ya dakatar da yakin neman zaben da yake inda tuni ya koma Dakar babban birnin kasar.
Rikicin wanda ya faru yau Litini tsakanin magoya bayan shugaban kasar Macky Sall da kuma na dan takaran jam'iyyar hammaya ta (PUR), Issa Sall, shi ne irinsa na farko tun bayan soma yakin neman zaben shugaban kasar dake tafe.
A ranar 24 ga watan Fabrairun nan ne al'ummar kasar ta Senegal ke kada kuri'a a babban zaben kasar, wanda a yayinsa, 'yan takara biyar zasu fafata wadanda suka hada da shugaban kasar mai neman wa'adi na biyu, Macky Sall, da Idrissa Seck, da Issa Sall, da kuma Madicke Niang sai kuma Usman Sonko.