Feb 13, 2019 06:57 UTC
  • Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama 3 A Kasar Masar Sun Bukaci A Dakatar Da Kisan Yan Adawa

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama guda ukku a kasar Masar sun bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da kisan yan adawa da kuma rungumi tattaunawa da fahintar juna da su.

Jaridar "Al-Qudsul Arabi" ta rubuta a shafinta na labarai kan cewa wasu kungiyoyin kare gakkin bil'adama ukku a kasar Masar, wadanda suka hada da "Egyptian Human Rights Front", "Justice Committee" da kuma  "Nidal Civil and Political Rights Institute," sun fidda wani rahoto na hadin guiwa inda a ciki suka bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da yanke hukuncin kisa kan yan adawa. 

Rahoton ya kara da cewa daga shekara ta 2013 ya zuwa yanzu kutuna daban-daban a kasar ta Masar, wadanda suka hada da kotunan soja ko na sauran jama'a sun yanke hukunce-hukuncen kisa kan yan adawa da dama. 

Har'ila yau rahoton ya kara da cewa kotunan kasar sun yanke hukunce-hukuncen kisa da dama a cikin wannan lokacin ba tare da yin adalci ko kuma bin ka'idojin kasa da kasa na shari'a ba.

Banda haka rahoton ya ce akwai mutane kimani dubu guda wadanda jami'an tsaron kasar ta Masar suka kashe a cikin wannan lokacin.

Tags