Feb 15, 2019 19:18 UTC
  • Majalaisar Dokokin Kasar Sudan Zata Fara Aikin Tsawaita Shugabancin Albashir

A yau ne majalisar dokokin kasar Sudan zata fara tattauna batun yiyuwan shugaban kasa mai ci Umara Hassan Albashir ya shiga takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2020 mai zuwa

Kamfanin dillancin laraban Spotnic majiyar majalaisar dokokin kasar ta Sudan tana cewa, an kaga komiti na musamman don gudanar da bincike kan yadda za'a yi wa kundin tsarin mulkin kasar koskorima don bawa shugaba Umar Hassan Albashir damar shiga takarar shugabancin kasar a zaben ashekara ta 2020.

A ranar lahadi mai zuwa ne ake saran za'a fara zaman tattaunawan, wanda zai hada da majalisar shura ta kasa da kuma majalisun lardunan kasar wadanda zasu tattauna batun da kuma fara aikin don tabbatar da hakan. 

Ana wannan ne a kasar Sudan a dai-dai lokacinda ake zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir tun ranar 19 ga watan Decemban da ta gabata, wanda kuma ya kai ga mutuawar mutane fiye da 40 a hannun jami'an tsaron kasar ta Sudan .

Shugaba Albashir dai yana shugabancin kasar Sudan tun shekara 1993, kuma a halin yanzu yana sun kara shiga takarar nean shugabancin kasar a shekara ta 2020.

Tags