An Kara Tsananta Tsaro A Kasar Algeria Kafin Zabubbukan Kasar.
(last modified Sun, 17 Feb 2019 19:13:13 GMT )
Feb 17, 2019 19:13 UTC
  • An Kara Tsananta Tsaro A Kasar Algeria Kafin Zabubbukan Kasar.

Jami'an tsaro a kasar Algeria wadanda suka hada da sojoji da 'yansanda sun kara tsananta tsaro a kasar Algeria a dai-dai lokacinda zabubbukan kasar yake karatowa.

Jaridar "Alkhabarul Yaumi" ta kasar Algeria ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun yi dafifi a dukkanin wuraren shiga birnin Alja'ir babban birnin kasar, suna kuma gudanar da da bincike a ababen hawa a wasu wurare a birnin.

A jiya Abasar ne kungiyoyi masu zaman kansu suka gudanar da zanga-zanga a cikin babban birnin Kasar Inda suke nuna adawarsu da sake tsayawar shugaban kasar Abdulaziz Butaflika takarar zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar a cikin wannan shekara.

A ranar 2 ga watan Febreru da muke ciki ne gamayyar Jam'iyyu da suke mulki a kasar ta Algeria suka bada sanarwan cewa shugaban kasa mai ci shi ne dan takararsu a zaben shugaban kasa mai zuwa. 

Abdulaziz Butafilika dai yana shugabancin kasar Algeria ne tun shekara ta 1999, sannan an zabe shi a kan kujerar shugabancin kasar har sau 4 tun lokacin. 

A ranar 18 ga watan Afrilu mai zuwa ne za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Algeria.