Tunisiya: Ana Cigaba Da Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35277-tunisiya_ana_cigaba_da_zanga_zangar_nuna_kin_jinin_gwamnati
Jaridar al-shuruq ta ba da labarin cewa; A Mutane masu yawa sun datse muhimmiyar hanyar da take isa yankin al-awamiriyah dake tsakiyar babban birnin kasar Tunis
(last modified 2019-02-19T12:25:03+00:00 )
Feb 19, 2019 12:25 UTC
  • Tunisiya: Ana Cigaba Da Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati

Jaridar al-shuruq ta ba da labarin cewa; A Mutane masu yawa sun datse muhimmiyar hanyar da take isa yankin al-awamiriyah dake tsakiyar babban birnin kasar Tunis

Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka fara Zanga-zanga a kasar ta Tunisiya  a yankin Barakah as-Sahil a yankin Kudu maso gabashin Tunis wanda ya kai ga mutuwar wani saurayi guda bayan taho mu gaba da jami'an tsaro

A gefe daya ma'aikatar cikin gidan kasar ta Tunisiya ta fitar da bayani da a ciki ta ce; saurayin ya yi doguwar suma ne, kuma jami'an kiwon lafiya sun yi kokarin ceto ransa amma ba su sami nasara ba

A cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata ma wani matashi ya kone kanshi domin nuna rashin jin dadinsa da tabarbarewar harkokin tattalin arziki a kasar