Feb 22, 2019 04:57 UTC
  • An Kame Sojojin Da Suka Zazzane Wata Mata A Chadi

A Kasar Chadi an kame wasu sojoji uku da aka nuno a cikin wani hoton bidiyo na zazzane wata mata.

Bayanai sun ce tuni aka garzaya da jami'an tsaron na ''gardi tsarki'' ko garde nationale zuwa N'Djamena babban birnin kasar inda zasu gurfana gaban kotu, kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta shaidawa masu aiko da rahotanni.

Bidiyon wanda akayi ta wallafawa a shafukan sada zumunta, a baya bayan ya dai nuna wasu sojoji kusa da wata motar soji, na zazzane wata mata da bulala, 

Saidai an bayyana cewa lamarin ya faru ne tun a shekara data gabata, kamar yadda matar ta shaidawa sashen BBC Afrique.

Matar ta ce kkwamandan sojin yankin ne yake nemanta, kuma ta shaida masa cewa tana da aure kuma mijinta soji ne kamar shi, don hakia ba zata iya biya masa bukata ba, amma ya nace kan hakan ta kiya.

Bayan hakan ne ya kulla mata sharri na zargin safara kwaya, wanda ya kai ga ssanya sojojin huda suka same ta tare da zazzane ta galaza mata, ciki har da jefa ta cikin laka. 

Faifan bidiyon dai ya janyo zazzafar muhawara da kuma toshin allah tsine a shafukan sada zuminta, inda kungiyoyin kare hakkin bila adama suka sukayi kiran da a dauki mataki kan duk masu azabtar da mata.

Tags