Ana Daf Da Kada Kuri'a A Babban Zaben Senegal
(last modified Sat, 23 Feb 2019 15:59:42 GMT )
Feb 23, 2019 15:59 UTC
  • Ana Daf Da Kada Kuri'a A Babban Zaben Senegal

A Senegal, al'ummar kasar miliyan 6,7 ne da suka cancanci zabe, zasu kada kuri'a a zaben shugaban kasar a gobe Lahadi 24 ga wata Fabarairu 2019.

Kawo yanzu an kiyasta cewa kahi, 97% na wadanda suka cancandi kada kuri'a sun riga sun karbi katin zabensu, wanda shi ne irinsa na farko da aka karbi zabe a wannan kasa ta Senegal a ecwar hukumomin kasar.

Kuma a yanzu haka bayanai na cewa kashi 3%, kwatancin mutum 185,000 wadanda basu karbi katinsu ba na fadi-tashin ganin sun karba domin kada kuri'a a zaben na gobe.

A jiya Juma'a ne dai aka kawo karshen yakin neman zaben, inda 'yan takara biyar ke fafatawa, ciki harda shugaban kasar Macky Sall, mai neman wa'adi na biyu.

Sauren yan takara da zasu fafata a zaben sun hada da Idrissa Seck, Issa Sall, Madicke Niang da kuma Usman Sonko.

Saidai a cen baya anyi ta korafi akan yadda wasu daga cikin sanannun fuskoki na 'yan siyasar kasar da suka hada da tsohon magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, da kuma dan tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade cewa da Karim Wade basu samu damar shiga zaben ba, kasancewar kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da takardun takararsu.