Ana Zaben Shugaban Kasa A Senegal
(last modified Sun, 24 Feb 2019 09:42:38 GMT )
Feb 24, 2019 09:42 UTC
  • Ana Zaben Shugaban Kasa A Senegal

Yau Lahadi ne al’ummar kasar Senegal ke kada kuri’a domin zaben shugaban kasa.

Mutane miliyan 6.7 ne da su ka cancanci kada kuri’a za su yi zabe.

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu kaso 97% na jumillar masu zaben sun karbi katunan zabe, wanda shi ne irinsa na farko da kasar za ta fara amfani da shi.

A shekaran jiya juma’a ne aka kawo karshen yakin neman zaben, inda 'yan takara biyar ke fafatawa, ciki har da shugaban kasar Macky Sall, mai neman wa'adi na biyu.

Sauren yan takara da zasu fafata a zaben sun hada da Idrissa Seck, Issa Sall, Madicke Niang da kuma Usman Sonko.