Gwamnatin Kasar Masar Tana Goyon Bayan Dunkulewar Kasar Iraqi
Shugaban kasar Masar Abdul Fattah Assisi ya ce gwamnatinsa tana goyon bayan dunkulewar kasar Iraqi.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Abdul fattah Assisi yana fadar haka a yau Lahadi a lokacinda yake ganawa da tokoransa na kasar Iraqi a birnin Sharm Shiekh da ke kasar ta Masar.
Assisi ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an sake gina kasar Iraqi bayan da aka kawo karshen kungiyar Daesh a kasar.
A nashi bangaren shugaban kasar Iraqi Barham Saleh ya bukaci kasashen larabawa su rungumi tattaunawa a tsakaninsu don warware dukkan matsalolin da ke shiga a tsakaninsu.
A yau ne aka fara taro tsakanin kasashen larabawa da turai a na kwanaki biyu a binrin sharm sheikh na kasar Masar. Inda ake saran batun ayyukan ta'addanci da yan gudun hijira ne zasu zama manya manyan agendan taron.