Senegal : Ranar Talata Za’a Fara Fitar Da Sakamakon Zabe
Feb 25, 2019 10:16 UTC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI a Senegal, ta ce sai nan zuwa ranar Talata ne take sa ran fara fitar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa jiya Lahadi.
Sanarwar da hukumar ta CENI ta fitar, ta ce za’a fara sanar da sakamakon ne a gobe a duk sassan kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da firaministan kasar ta Senegal, ya firta cewa, shugaban kasar Macky Sall ne mai ya lashe zaben da kasha 57% na yawan kuri’un da aka kada.
A yayin wani taron manema labarai da suka gudanar manyan ‘yan takara adawa na kasar, sun yi gargadi akan bayyana duk wani sakamakon zabe da yake nuna shugaban kasar ne ya yi nasara.
Tags