Feb 25, 2019 15:07 UTC
  • Zimbabwe Ta Rage Darajar Kudin Kasarta Saboda Matsalolin Tattalin Arziki

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar rage darajar kudin kasar da nufin tunkarar matsalolin tattalin arziki da kasar take fama da su.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, sakamakon matsaloli na tattalin arziki da suka yi wa kasar Zimbabwe katutu, hakan ya sanya gwamnati ta dauki matakin kara karya darajar kudin kasar, da nufin tayar da komadar tattalin arzikin kasar.

Tun a cikin shekara ta 2009 ce tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya shiga cikin wani mawuyacin hali, sakamakon takunkumai na tattalin arziki da Amurka ta kakaba wa kasar da kuma kasashen yammacin turai a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

Sabon shugaban kasar ta Zimababwe Emmerson Mnangagwa yana daukar matakai na fuskantar wannan matsala, wanda kuma karya darajar kudin kasar na daga cikin irin sabbin matakan da yake dauka a halin yanzu.

 

 

 

 

Tags