ECOWAS Ta Yaba Da Yadda Zaben Senegal Ya Gudana
(last modified Tue, 26 Feb 2019 06:58:31 GMT )
Feb 26, 2019 06:58 UTC
  • ECOWAS Ta Yaba Da Yadda Zaben Senegal Ya Gudana

Tawagar masu sanya ido ta kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika na yamma, wato ECOWAS, ta yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a Senegal.

Da yake sanar da hakan, shugaban tawagar masu sanya ido na ECOWAS a zaben, tsaohon shugaban kasar Benin, Boni Yayi, ya ce zaben shugaban kasar na Senegal, ya gudana cikin lumana, da'a da kuma nuna kishin kasa, da kuma yadda aka fito dafifi aka kada kuri'a a zaben, ta tare da wata matsala ba.

Tawagar ta masu sanya ido a zaben ta kuma bukaci dukkan 'yan siyasar kasar dasu kai zuciya nesa, kuma duk wanda ya ji ba'a masa daidai ba to ya kai kara gaban shari'a kamar yadda dokokin kasar suka tanada.Masu sanya

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ke ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka kada kuri'arsa a ranar Lahadi data gabata.