An Dauki Kwararen Matakan Dakile Zanga-zanga A Sudan
(last modified Tue, 26 Feb 2019 07:17:59 GMT )
Feb 26, 2019 07:17 UTC
  • An Dauki Kwararen Matakan Dakile Zanga-zanga A Sudan

Gwamnatin Sudan ta dauki wasu kwararen matakai da ake ganin cewa na dakile duk wani yunkuri na ci gabda zanga-zanagr adawa da gwamnatin kasar.

Matakan da gwamnatin ta dauka sun hada da hana taruka na jama'a da zanga-zanga da yajin aiki, kana kuma sun haramta duk wani yajin aiki a duk fadin kasar.

An kuma sanar da girka kotunan shari'a na gaggawa, tare kuma da baiwa masu shigar da kara hurimin tube rigar kariya ga manyan jamia'ai kamar 'yan majalisar dokoki da kuma manyan sojoji idan har akwai zargi.

Sabon matakin kuma ya baiwa dukkan rundunonin jami'an tsaro damar gudanar da bincike, samame, takaita zurga-zurga ta mutane da kuma ta ababen hawa da kuma cafke duk wani mutum da ake zargi da keta dokar ta bacin da aka kafa a kasar.

Wanann dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir ya rusa gwamnatin kasar,  da kuam kafa dokar ta baci a duk fadin wannan kasar ta Senegal a ranar Juma'a data gabata.