Uganda Ta Soki Rwanda Saboda Rufe Kan Iyakar Kasashen Biyu
Kasar Uganda ta soki makwabciyarta Rwanda saboda rufe kan iyakar kasashen biyu.
Kakakin gwmanatin kasar Uganda Ofwono Opondo ya bayyana cewa; matakin da gwamnatin ta kasar Rawanda ta dauka na rufe kan iyakoki ya samo asali ne daga rashin fahimta, wanda kuma ya zuwa yanzu babu wani bayani da ya fito daga gwamnatin kasar ta Rawanda.
Kakakin gwamnatin ta Uganda ya kara da cewa; Rwanda ta rufe kan iyakarta ne ba tare da yin wani bayani ba, amma idan ta cigaba to ita ma Ugandan za ta rufe nata kan iyakar.
A nata gefen, gwamnatin kasar Rwanda ta bakin ministan harkokin waje, Richard Sezibera, gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne saboda yadda Uganda ta ba da mafaka ga masu adawa da gwamnatin shugaba Paul Kagami, sannan kuma suke gudanar da ayyukan da ba su dace ba daga kasar.
A cikin watannin bayannan alaka a tsakanin kasashen Uganda da Rawanda ta yi tsami saboda yadda suke zargin juna da baiwa ‘yan adawa mafaka.