Burkina : An Kaddamar Da Mutum Mutumin Martaba Thomas Sankara
A Burkina Faso, a karon farko an kafa mutum mutumin martaba tsohon shugaban kasar mirigayi Thomas Sankara, wanda ya jagoranci gwagwarmayar samarwa da 'yan kasar 'yanci.
An dai kaddamar da mutum mutimin ne yau Asabar a daura da bukin nuna fina finan Afrika na FESPACO.
Tsohon shugaba Sankara wanda aka kashe a cikin shekara ta hudu ta mulkinsa yana daga cikin gwarzayen Afrika kuma 'yan mazan jiya wadanda suka kafa ra'ayin kishin Afrika.
Daga cikin mutanen da suka halarci bikin yaye kalabin mutum mutumin na Sankara, harda shugaban kasar ta Burkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Rawlings.
Mutum mutumin mai tsawan mita 5 an gina shi ne a dandalin cibiyar kasar ta gwagwarmaya inda a nan ne aka kashe Sankara a ranar 15 ga watan Oktoba 1987 a wani juyin mulki wanda amininsa kuma abokin aikinsa Blaise Campaore ya shirya.
An dai shafe kusan shekaru 27 ana neman haske kan kisan Sankara saidai hakan bata yi ba a lokacin mulkin Blaise Compaure, wanda daga bisani ya bar mulki a ranar 31 ga watan Oktoba 2014 sakamakon boren jama'ar kasar na kin jinin gwamnatinsa.