An Gano Wasiku Wadanda Aka Shafa Masu Goba A Tunisia
(last modified Sun, 03 Mar 2019 07:34:34 GMT )
Mar 03, 2019 07:34 UTC
  • An Gano Wasiku Wadanda Aka Shafa Masu Goba A Tunisia

Ma'aikatar cikin gida na kasar Tunisia ta bada sanarwan cewa ta gano wasu wasiku guda 19 wadanda aka shafa masu sinadarin guba da nufin halaka wasu fitattun yan siyasa a kasar

Kamfanin dillancin labaran Spotnic ta nakalti jami'an ma'aikatar suna fadar haka a jiya Asabar, sun kuma kara da cewa wannan wani sabon salo ne na ayyukan ta'addanci a kasar, da nufin cutar da manya-manyan yan siyasa, da shuwagabannin kafafen yada labarai na kasar.

Ma'aikatar ta ce wannan shi ne sabon salo na shuwagabannin yan ta'adda a kasar kuma dole ne ma'aikatar ta samar da shiri na musamman don kalubalantarshi. Daga karshe ma'aikatar ta bukaci mutanen kasar da su bada rahoto ga jami'an tsaro a duk lokacinda suka gano wata wasika wacce suke kokwanton zata iya zutar da mutane.

Majalisar dinkin duniya dai ta bada sanarwan cewa yan ta'adda yan asalin kasar Tunisia sun kai dubu 5 a halin yanzu, sannan mafi yawansu suna aiki tare da kungiyoyin yan ta'adda a kasashen Iraqi da Siriya ne. Amma bayan fatattakarsu daga aka yi a wadannan kasashe a halin yanzun sun tarwate zuwa kasashen duniya da dama. Daga ciki har da ita kasar Tunisia