Kasar Rwanda Ta Tura Sojoijin Zuwa Kan Iyakar Kasar Da Kasar Uganda
Kasar Rwanda Ta Tura Sojoijinta Zuwa Kan Iyakar Kasar Da Kasar Uganda.
Tura sojojin da Rwandan ta yi, yana zuwa ne a daidai lokacin da alakar diplomasiyya ta kasashen biyu take kara lalacewa.
Wata kafar watsa labaru ta kasar Uganda ta ce ana iya tsinkayar sojojin na Rwanda daga tuddan Mkaniga, Byumba da kuma Buganza wadanda suke a cikin kasar ta Uganda.
Rahoton ya kara da cewa; Ana kuma iya hango sojojin na Rwanda suna gudanar da sintiri akan iyakar kasashen biyu, da ga yankin Chanika da ke gundumar Kisoro na kasar.
Mahukuntan kasar Uganda sun ce ba su ga dalilin da zai sa Rwanda ta tura sojojin nata akan iyakar kasashen biyu ba.
A shekarar 2000 kasashen biyu sun yaki juna a kasar Demokradiyyar Congo, wanda ya yi sanadiyyar kashe fiye da mutane 1000
A makon da ya gabata ne dai kasar Rwanda ta sanar da rufe kan iyakarta da Uganda bisa zargin da take yi wa Kamfala da bai wa ‘yan adawar kasar mafaka.