Mar 05, 2019 13:19 UTC
  • An Sallami Jagoran 'Yan Adawa Na Sudan

Hukumomi a Sudan sun sallami jagoran 'yan hamayya na kasar, wanda aka cafke kwanaki kadan bayan zanga zangar tsadar rayuwa da kuma kin jinin gwamnati.

Omar el-Digeir, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Sudan Congress Parti, an cafke shi ne a ranar 29 ga watan Disamban bara, kwanaki goma bayan zanga zanga data bazu a kasar, biyo bayan matakin gwamnati na kara kudin bredi a daidai lokacinda kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.

A wata sanarwa data fitar jam'iyyar ta tabbatar da sakin jagoran nata, bayan shafe watanni biyu ana tsare dashi.

A nasa bangare madugun 'yan adawan na Sudan, Omar el-Digeir, ya bayyana a shaffinsa na twitter cewa jam'iyyar ta yunkuri anniyar ci gaba da kokowa har sai ta cimma burinta.

Bayanai daga kungiyoyi masu zaman kansu sun nuna cewa daruruwan masu zanga zanga ne da 'yan adawa aka cafke tun bayan soma zanga zangar a farkon watan Disamba.

A ranar 22 ga watan Fabrairu, shugaba Umar Hassan El Bashir, ya kafa dokar ta baci ta tsawan shekara guda a duk fadin kasar, tare da haramta gangami ko zanga zanga ba tare da samun izini ba, matakin da ake wa kallon wani salo na murkushe boren da ake a kasar.

Tags