'Yan Tawayen Miski A Chadi Sunyi Biris Da Kiran Gwamnati
(last modified Wed, 06 Mar 2019 05:45:23 GMT )
Mar 06, 2019 05:45 UTC
  • 'Yan Tawayen Miski A Chadi Sunyi Biris Da Kiran Gwamnati

'Yan tawayen Miski a yankin arewa maso yammacin Chadi, sun yi watsi da kiran da gwamnatin kasar ta yi ga dukkan 'yan tawayen kasar na su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Molly Sougui ya fitar, ya ce ba za su amince da kiran gwamnatin ba, ba tare da gwamnatin ta samar masu da mafita akan abin da  ya tilasta masu daukar makamai ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan rangadin da ministan tsaron cikin gdian kasar ya yi ne a yankin, tare da sanar da cewa dukkan 'yan tawayen su ajiye makamai, tare da haramta duk wasu ayyukan neman zinari a yankin, dake fama da rikice rikice tsakanin sojojin kasa da masu bidar zinariya.

'Yan tawayen dai na neman gwamnati ta ba su damar gudanar da ayyukan neman zinari a yankin na Tibesti.

Saboda rikice rikicen da ake fuskanta a yankin ne Gwamnatin kasar ta  Chadi ta sanar da rufe kan iyakarta da kasar Libiya, har sai abin da hali ya yi, saboda a cewarta yadda yankin ya zama wata matattara ta 'yan daba, 'yan ta'adda da duk wasu masu aikata muggan laifuka.