Mar 06, 2019 13:47 UTC
  • Senegal : Majalisar Tsarin Mulki Ta Yi Na'am Da Zaben Macky Sall

Majalisar tsarin mulki a Senegal, ta yi na'am da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 24 ga watan Jiya, wanda shugaba Macky Sall, ya lashe a wani wa'adin mulki na biyu.

Saidai majalisar ta yi dan gyara a sakamakon zaben, inda daga kashi 58,27%, ta ce shugaba Macky Sall ya samu kashi 58,26% ne na yawan kuri'un da aka kada.

Sakamakon wanda shi ne na dindin-din ya kuma ce, dan takara Idrissa Seck, ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kashi 20,51%, sai kuma Usman Sonkodake biye masa da 15,67%, a yayin da shi kuwa dan takara Issa Sall, wanda ya samu kashi 4, 07%, sai daga karshe, Madické Niang wanda ya samu kashi 1, 48% na jimilar kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar.

Saidai dukkan 'yan takaran adawan da suka fafata da shugaba Macky Sall, sunyi fatali da sakamakon zaben, saidai basu dau matakin garzayawa majalisar tsarin mulkin kasar ba don kalubalantar zaben.

Tags