Ghana Na Bikin Cika Shekaru 62 Da Samun 'Yancin Kai
A Yau ne kasar Ghana take bikin cika shrekaru 62 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar Birtaniya
A cikin sakon zagayowar wannan rana ta samun ‘yanci, shugaban kasar ta Ghana Akufo-Addo ya skae jaddada wani sashe na jawabin da Kwame Nkurmah ya yi namun ‘yanci shekaru 62 da su ka gabata.
Shugaba Akufo-Addo ya ce; A karshe yaki ya zo karshe, Kasar da kuke kauna Ghana ta sami ‘yanci. Za mu kare ‘yancinmu da digon jininmu na karshe.”
Shugaban na kasar Ghana ya yi jawabinsa ne a wurin bikin tunawa da zagayowar lokacin da kasar ta sami ‘yanci, a garin Tamale da ke gundumar Arewa.
An gabatar da faretin soja da sauran jami’an tsaro da kuma dalibai a cikin filin wasanni na Aliu Mahama dake cikin birnin Tamale.
Wannan ne dai karon farko da aka gabatar da bikin samun ‘yancin kasar a daya daga cikin gunmumomin kasar, maimakon babban birnin kasar Accra.
Dubun dubatar mutane ne daga bangarori daban-daban na rayuwa su ka sami halartar gagarumin bikin a cikin filin wasannin na Aliu Mahama.
Daga cikin manyan bakin da su ka halarci bikin da akwai shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Isufu.