An Hallaka Sojoji 6 A Kasar Mali
Rundunar tsaron kasar Mali ta sanar da mutuwar sojojinta shiga sanadiyar tashin Nakiya a tsakiyar kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto dakarun tsaron kasar Mali na cewa akalla sojojin kasar shida ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin nakiya da aka dasa a kan hanyar motocin sojoji a lardin Mopti dake tsakiyar kasar.
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne a jiya Talata,kuma tuni gwamnatin ta Mali ta yi allawadai da harin tare da bayyana shi a matsayin harin ta'addanci.
Tun a shekarar 2014 ne kasar ta Mali ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda dake da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta Alqa'ida.
A makon da ya gabata ma, saktare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ja hankali kan yadda al'amuran tsaro ke kara tabarbarewa a kasar ta Mali, inda ya ce hare-haren ta'addancin da ake kaiwa Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da Dakarun kasar Mali gami da Dakarun kasa da kasa na kara karuwa.