Za'a Kafa Sabuwar Gwamnati A Sudan
Kafar watsa labaran Arabie News ta nakalto Mohamed Tahir Ayala Piraministan kasar Sudan a wannan Laraba yayin da yake mayar da martani kan ci gaba da kin jinin gwamnatin Omar al-Bashir na cewa nan ba da jimawa ba za a kafa sabuwar gwamnati a kasar.
A cewar Piraministan na Sudan sabuwar gwamnatin za ta kumshi ministoci 21, inda Al Dirdiri Mohamed Ahmed zai riki mikamin ministan harakokin wajen kasar, sannan Mohamed Ahmed Salem ya riki mikamin ministan shari'a na kasar.
A kwanakin da suka gabata ne, Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan ya kori Piraministan kasar tare da maye gurbinsa da Mohamed Tahir Ayala.
Tun a ranar 19 ga watan Dicembar shekarar da ta gabata ce, al'ummar kasar Sudan suka fara gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da hauhauwar farashin kayan masrubi na yau da kulun musaman ma Biredi da man fetir a kasar, daga baya kuma zanga-zangar ta rikede zuwa neman shugaba al-Bashir ya yi murabus.