Mar 24, 2019 05:41 UTC
  • Amurka Ta Sake Kakabawa Jami'an Hukumar Zaben Congo Takunkumi

Amurka ta sake kakabawa manyan jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI, a DR Congo takunkumi.

Amurka na zargin jami'an da sabawa harkokin zaben da ya gudana a kasar ta D R Congo.

Mutanen da aka kakabawa takunkumin sun hada da shugaban hukumar ta CENI, Corneille Nangaa, da kuma mataimakinsa Norbert Basengezi, da kuma wani masharwacin hukumar mai suna Marcellin Mukolo Basengezi.

Takunkuman sun hada da haramta wa jami'an sanya kafa a Amurka, da toshe kaddarorinsu.

A ranar 22 ga watan Fabrairu da ya gabata ne, Amurka ta kakabawa jami'an da takunkumin hana shiga kasar a matakin farko.

Tags