Kasar Beljika Ta Karbi Ragamar Jagorancin Sojojin Tarayyar Turai A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i361-kasar_beljika_ta_karbi_ragamar_jagorancin_sojojin_tarayyar_turai_a_mali
Kasar Beljika ta karbi ragamar jagorancin sojojin tarayyar Turai wadanda suke aikin
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 06, 2016 03:02 UTC
  • Kasar Beljika Ta Karbi Ragamar Jagorancin Sojojin Tarayyar Turai A Mali

Kasar Beljika ta karbi ragamar jagorancin sojojin tarayyar Turai wadanda suke aikin

Kasar Beljika ta karbi ragamar jagorancin sojojin tarayyar Turai wadanda suke aikin tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar Mali. Kamfanin dillancin labarai AFP ya bayyana cewa a jiya Jumma'a ne jami'an sojojin kasar ta Beljika suka bayyana haka. Sun kuma kara da cewa tun farkon wajen Jeneru na wannan shekara ta 2016 kasar Beljika ta karbi ragamar jagorancin rundunar ta tarayyar Turai daga hannun kasar Jamus kuma za'a ci gaba da aikin bada horo da kuma tarbiyya ga sojojin kasar ta Mali a arewacin kasar. Sanarwan ya kara da cewa kasar beljika ta kara yawan sojojinta a kasar ta Mali daga 90 zuwa 175 bayan da ta karbi ragamar jagorancin rundunar. Kasashen Turai 25 ne suke da sojoji a arewacin kasar ta Mali.