Ganawar Shugaba Buhari Na Najeriya Da XI Jinping Na China
Shugabannin kasashen Najeriya da na China sun gana a jiya a birnin Beijin, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen biyu za su aiki a bangarori na ci gaba, inda ya ce China za ta taimaka ma Najeriya a bangarori na bunkasa harkokin tattalin arziki da inganta masana'antu da ayyukan hakar mai da hakar ma'adanai noma da saraunsu.
A nasa bangaren shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa, tun bayan gudanar da zaman da aka yi tsakanin China da kasashen Afirka a karshen 2015 a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, an samu gagarumin ci gaba ta fuskar dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
Yanzu haka dai China ta ba wa Najeriya bashin kudade kimanin dala biliyan 6 domin inda ayyukan gine-gine da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, yayin da kuma wasu ke danganta tafiyar baki daya da cewa tana da alaka ne da neman wannan bashi, domin cike gibin da aka samu kasafin kudin Najeriya na 2016.