Mali : Nakiya Ta Hallaka Sojojin Faransa Uku
-
wani sojan Faransa a arewacin Mali
Gwamnatin Faransa ta sanar da mutuwar wasu sojojin ta uku bayan da motar su ta taka nakiya a kasar Mali.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar yau Laraba ta ce biyu daga cikin sojojin sun mutu ne a sakamakon munanen raunukan da suka samu bayan da motar tasu ta taka nakiya a kusa da garin Tessalit dake arewacin Mali.
Tun da farko dai kasar ta Faransa ta sanar a jiya da mutuwar sojan ta daya tare da raunanar wasu uku na daban wanda biyu daga cikin su sun samu munanen raunuka.
Shugaban kasar ta Faransa Francois Hollanda ya nuna matukar damuwar sa dangane da aukuwar lamarin.
kasar Faransa dai na da rundinar sojin ta mai suna (Barkhane) dake kunshe da sojoji 3,500 a kasashe biyar na yankin Sahel da suka hada da Burkina faso, Mali, Mauritaniya, Nijar da kuma Chadi, da nufin kawar da ayyukan kungiyoyi masu kaifin kishin addini.